Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Mista Peter Dike da ake zargi da hallaka matarsa ta hanyar caka mata wuka a gidansu da ke Unguwar Oke-Ira Ilogbo Eremi Marogbo da ke Jihar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a jiya Alhamis ta ce abin zargin ya hallaka matar tashi ne bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu a ranar Larabar da ta gabata.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Benjamin Hundeyin ya ce bayan samun rahoto da jami’ansu na yankin Morogbo suka yi kan lamarin su nufi gurin tare da kama wanda ake zargi.

Kakakin ya ce bayan kama wanda ake zargin ya amsa dukkan laifunka, inda kuma aka ajiye gawar matar tashi a dakin ajiye gawarwaki na babban asibitin Badagry, daga bisani kuma a mikata ga sashin binciken manyan laifuka na Jihar.
