Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga cikin mutane 347 da aka kama da laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a fadin Kasar, an gurfanar da mutane 143 a gaban kotu bisa samunsu da laifin.

Ministan Ma’adanai na Kasa Dele Alake ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce hakan na daga cikin himmar gwamnatin tarayya na ganin a hukunta mutanen da aka kama da laifin.
Kama mutanen na zuwa ne bayan samar da wata rundunar tsaro a shekarar 2024 da ta gabata, da za ta yi aikin kawo karshen masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba Kasar.

Acewar Ministan rundunar da aka kafa ta samu nasarar kwato guraren hakar ma’adanai guda 98, ya yin da ta gano wasu haramtattun guraren guda 457, tare kuma da kwace wasu gurare da wasu suka mamaye fiye da shekaru 10 ba tare da izini ba.

Bugu da kari ya ce a halin yanzu gwamnatin ta tarayya na shirye-shiryen fadada aikin rundunar zuwa Jihohin Kasar, da kuma yin amfani da na’urori domin ganin an sanya idanu akan masu hakar ma’adanan.
Kazalika ya ce dakile dabi’ar hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba hakan zai taimaka matuka wajen kara samar da kudaden shiga a bangaren ma’adanan.
Ministan ya kuma yaba hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon Kasa ta EFCC bisa namijin kokarin da ta yi wajen gurfanar da masu laifin a gaban kotu.
Sannan ya ja kunnen masu dabi’ar hakar ma’adanan da su kauracewa yin hakan ko kuma su fuskanci hukunci.