Dakataccen gwamnan Jihar Rivers Siminalayi Fubara ya nesanta kansa daga wasu hotuna da bidiyoyi da ke yawo cewa an fasa bututun mai a wasu gurare a jihar.

A wata sanarwa da dabban sakataren yada labaran Fubara Nelson Chukwudi ya fitar a yau Litinin, ya ce babu gaskiya a cikin batun fasa bututun mai a guraren da ake zargi.

Nelson ya ce mutane da ake bayyana cewa an fasa bututun mai a yankunansu sun fito sun musanta batun, inda ya ce dukkanin kayayyakin gwamnati da ke yankunan suna nan cikin kulawa da kariya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Fubara ba zai lamunci yunkurin tayar da zaune tsaye ba, inda ya ja kunnen masu yada irin wadannan rahotanni marasa tushe balle makama.

Acewarsa Fubara ya kuma nesanta kansa daga kowacce kungiya ta ‘yan bindiga ko wasu masu tayar da zaune tsaye a jihar ko yankin Niger Delta, yana mai cewa ba zai taba goyan bayan wata kungiya ba, burinsa ce kullum tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Sanarwar ta bukaci da hukumomin tsaro su dauki matakin da ya kamata a kai domin gano masu yada bidiyoyi tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Rahotannin dai na nuni da cewa wasu gurbatattun mutane ne ke kokarin danganta wadannan bidiyoyi da magoya bayan Siminalayi Fubara.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: