Babban sufeton ƴan sandan Najeriya ya gargadi jami’ansa a kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sanda Olumuyiwa Adejobi ya rabawa manema labarai jiya Lahadi.
Sufeton ya ce za a hukunta duk jami’in da aka samu da tsare wani ko wata a ko ina a Najeriya tsarewar da ta saɓawa doka.

A cewar sufeton, za su ci gaba da aikin tabbatar da tsare yancin dan adam da kuma bin matakan da su ka dace wajen tsare wanda ake zargi.

Sannan ya ce ya zama wajibi jami’an su fahimta tare da mutunta dokar kare yancin dan adam.
A cewarsa, tsare mutane ba bisa ƙaida ba na kawar da amincewar da jama’a ke yi wa jami’an.
A sakamakon haka ya ce ba za su lamunci duk wani abu da zai kawo naƙasu ga aikin ba, kuma za su hukunta duk wanda aka samu da cin zarafin dan ƙasa.