Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya ya nada Alhaji Bappa Ibrahim Muhammad a matsayin hakimin Gombe a karkashin Majalisar Masarautar Jihar.

Alhaji Bappa da ne ga Marigayi Sarkin Gombe Alhaji Umaru Muhammad Kwairanga, ya yin da ya kasance Kawu ga Sarkin Gombe na yanzu Alhaji Abubakar Shehu Abubakar na lll, kuma kafin nadin shi ya shi ya shafe shekaru sama da 23 ya na rike da Hakimin Jalo Waziri.
Gwamnan ya nada shi ne bayan rasuwar Alhaji Abdulkadir Abubakar hakimin na Gombe tun a shekarar 2023 da ta gabata.

A yayin mika takardar nadin nashi Mataimakin gwamnan Jihar Dr Manassah Daniel Jatau, ya bukaci da Alhaji Bappa da ya kasance mai adalci, zaman lafiya, tare da kiyaye martabar al’ummarsa.

Sannan Jatau ya bayyana cewa gwamnatin Jihar ta fatan sabon hakimin zai dora daga kan manufofin da su ci gaba da tabbatar da hadin kai a tsakanin al’umma, da kuma ci gaban Masarautar Jihar.
Kafin nadin nashi Alhaji Bappa ya kasance sananne ne akan tafiyar da Masarauta da kuma al’umaran da suka shafi al’umma, inda kuma a bayan shi ne daraktan karkokin gudanarwa da kudi na Majalisar Dokokin Jihar, tare kuma da bayar da gudummawar a banmgarori daban-daban na Jihar.