Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar ya ce Najeriya ta ci gaba da samo hanyar da za ta kawo karshen matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a fadin Kasar.

Badaru ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da aikin horas da jami’an sojin Najeriya 800 a Jihar Kaduna domin karfafa musu gwiwa wajen yaki da ‘yan ta’adda a Kasar, yayin da daga bisani wasu 800 kuma su biyo baya.
Ministan ya kara da cewa jami’an su ne kaso na farko na jami’ai 2,400 da Najeriya za ta horas tare da hadin gwiwar kwararru daga kasashe ketare bakwai.

Alhaji Badaru ya ce za a horas da jami’an tsaron ƙasar ne kan sababbin dabarun yaki, irin wanda ba a saba gani ba, wanda hakan zai bayar da damar gudanar da ayyuka na musamman, tare da gaggauta kubtar da waɗanda aka yi garkuwa da su tare da yaƙi da rashin tsaro da kwarewa.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin ta karɓi dukkanin ƴan bindigar da suke son tuba tare da ajiye makamai, ya na mai cewa Sai dai ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta dunga neman ‘ƴan ta’adda ba domin yin sulhu, inda ya ce ba za su lamunci ‘yan bindiga suna ci gaba da hallaka al’umma ba.
Ministan ya bayyana cewa ana ci gaba da samun kwanciyar hankali a wasu yankunan Kasar sakamakon yadda gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro a fadin Kasar.
