Ƙungiyoyin ma’aikatan jiragen sama na Najeriya sun yi barazanar rufe dukkan filayen sauka da tashin jiragen sama na Kasar daga ranar 31 ga watan Maris din nan da muke ciki.

Ma’aikatan sun yi barazanar rufe filayen jiragen Kasar ne, tare da nema gwamnatin tarayya da ta dauki matakin kora ga jami’in hukumar hana fasa kauri ta Kasa kwastam da ake zargi da hannu wajen cin zarafin daraktan tsaro a hukumar kula da filayen jiragen sama ta Kasa.

A wata sanarwa da gamayyar kungiyoyin suka fitar sun nuna rashin aminta da abin jami’in na Kwastom ya aikata.

Sannan kungiyoyin sun kuma nuna rashin jindadunsu bisa yadda ake samun yawaitar cin zarafin ma’aikatan hukumar kula da filayen jiragen saman Kasa.

A Bangaren hukumar ta kwastam ta ce rashin fahimtar da ya faru tsakanin jami’inta da Ma’aikatan filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas ya ce rashin fahimta ne.

Mai magana da yawun hukumar na Kasa Abdullahi Mai Wada Aliyu ya ce hukumar na kokarin ganin ta hada kai tsakanin bangaren, don ci gaba da gudanar da aiki yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: