Wata kungiya mai rajin tabbatar da shugabanci nagari a Jihar Zamfara CDD ta yi kira ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya ayyana dokar tabaci a Jihar Zamfara.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a jiya Litinin a birnin tarayya Abuja.
Shugaban kungiyar Ibrahim Yakubu ya ce wasu matakai da gwamnatin Zamfara ke dauka na barazana ga dimokuradiyya da kuma zaman lafiya a fadin jihar.

Kungiyar ta nuna damuwarta akan yadda matsalolin tsaro da na tattalin arziki ke ƙara ta’azzara a jihar Zamfara.

Daga cikin abubauawan da kungiyar ta zayyano sun hada da dakatar da ƴan Majalisar Dokoki, taɓarɓarewar tsaro, da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.
Kungiyar ta kuma nuna takaicin kan dakatar da mambobi 10 na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara har na tsawon watanni 13 saboda sun bisa nuna ɓacin ransu kan matsalar tsaro a Jihar.
Kungiyar ta yi zargin matakan gwamnatin Dauda Lawal na PDP sun kara lalata harkar tsaro a jihar, Inda ta ce tana zargin ana gudanar da hakar zinare da sauran ma’adanai ba bisa doka ba, lamarin da ke barazana ga tattalin arzikin jihar.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin Tarayya na da hakkin daukar matakan gaggawa don tabbatar da doka da oda a Zamfara.