Gwamnan riƙo na jihar Rivers Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe ya sauke dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa na jihar ba tare da ɓata lokaci ba.

A wata sanara da shugaban ma’aikatan jihar ya fitar jiya Laraba gwamnan ya kuma sauke dukkan masu riƙe da muƙamai a jihar

Daga cikin waɗanda saukewar ta shafa akwai sakatarn gwamnati jihar, shugaban ma’aikatan jihar, kwamishinoni, masu ba da shawara, mataimaka na musamman da shugabannin hukumomi.

Saukewar kuma ta fara ne daga jiya Laraba kamar yadda sakataren gwamnatin gwamnan riƙon ya bayyana.

Gwamnan ya umarci waɗanda aka sauke su muƙa muƙaman ga sakatarorin dindindin a maaikatun ko wani babban mai muƙami.

Matakin da gwamnan ya ɗauka ya yi ne mako guda bayan naɗashi a natsayin gwamnan riƙo bayan da shugaban ƙasa ya sanar da sanya dokar ta ɓaci a jihar tare da dakatar da gwamna, mataimakiyarsa da yan majalisar dokokin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: