Majalisar wakilan Najeriya ta jingine kudurin dokar janye kariya ga mataimakin shugaban Kasa da gwamnoni da mataimakansu a Kasar.

Sannan kuma Majalisar ta dakatar da amincewa da kudurin da ke neman soke hukuncin kisa ga masu laifi a Kasar.
Ƙudurorin biyu na daga cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a Majalisar a jiya Laraba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da kudurin nema janye kudurorin.

Ya yin da kuma Mataimakin mai magana da yawun majalisar Benjamin Kalu ya bayyana cewa Malajisar ta janye kudurorin ne domin bayar da damar gudanar da muhawara akan ƙudurorin.
Kudurin dai na daga cikin manyan kudurori da Majalisar ke yin nazari akai, duk a wani bangare na yin kwaskwarima a kundin tsarin mulkin Kasa na shekarar 1999.
Rahotannin sun bayyana cewa Majalisar ta janye kudurorin ne bayan da gwamnonin Jihohin Kasar, sun soki kudurin da ke neman cire musu rigar kariya.