Majalisar wakilan Najeriya ta tsallake karatu na biyu kan kudurin da zai haramtawa ‘yan takarar shugaban Kasa, da na gwamnan masu shekaru sama da 60 tsayawa takara.

A zaman Majalisar na yau Alhamis, da kudurin ya tsallake karatu na biyu, bayan da dan Majalisar Hon Ikeagwuonu Ugochinyere ya dauki nauyin kudurin da ke bukatar canza wasu bangarori na kudin tsarin mulkin Kasa na shekarar 1999.

Rahotanni sun bayyana cewa da zarar kudurin ya tsalle karatu na uku, kuma shugaban Kasa ya sanya hannu akansa, hakan zai sauya fasalin tsayawa takara a Kasar.

Daga cikin abubuwan da kudurin ya kunsa sun hada da, dukkan wanda ya haura shekaru 60 da haihuwa b azai tsaya takarar shugaban Kasa ba, ko gwamna a Kasar.

Sannan kuma wajibi dukkan dan takara ya kasance ya mallaki shedar digirinsa na farko a bangaren da ya fi kwarewa akai, a matsayin mafi karancin takardar karatu.

Ya yin da kuma kudin ya bukaci yin gyara a sashe na 131 na kudin tsarin mukin Kasa, na bukatar iyaknce shekaru ga kowanne dan takarar shugaban Kasa, tare da sashi na 177 ga gwamomin Jihohi.

Baya ga wannan kuduri majalisar ta kuma amince da wasu kudurori daban-daban da suka shafi ci gaban Najeriya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: