Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi Allah-wadai da kisan rashin imani da aka yiwa wasu ‘yan Arewa 16 da ke kan hanyarsu ta dawowa Kano a Jihar Edo.

Kwankwaso ya nuna bacin ransa kan lamarin ne ta cikin wata wallafa da ya fitar a yau Juma’a, yana mai cewa lamarin abin takaici ne da ke kara bayyana munin daukar doka a hannu.

Kwankwaso ya ce kowanne dan Kasa na da ‘yancin yin tafiye-tafiye ba tare da cin zarafi ko kuma fuskantar wata barazana ba.

Sanata Kwankwaso ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin, tare kuma da hukunta dukkan wanda aka kama da hannun a cikin kisan mutanen.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma kika sakon ta’aziyyar ga gwamnatin Jihar Kano, ‘yan uwa da iyalan wadanda lamarin shafi, tare da neman gafara da rahma a garesu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: