Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku daga cikin mutane 33 wadanda suka kamu da cutar sankarau a Jihar.

Kwashinan Lafiya na Jihar Dr Habu Dahiru ne ya tabbatar da hakan a jiya Alhamis a lokacin da yake yiwa manema labarai karin bayani akan samuwar cutar a Jihar.

Dr Habu ya bayyana cewa sun samu rahoton mutane 53 da ake zargi sun kamu da cutar a Kananan hukumomin Kaltungo, Yamaltu Deba, Billiri, da kuma Gombe.

Kwamishinan ya ce daga cikin mutane hudu da ake zargin sun kamu da cutar a garin Shongom uku daga cikinsu na dauke da cutar.

Sannan ya ce a Kananan hukumomin Dikku, da Nafada kuwa kowanne an samu mutum dai daya, amma ba tabbatar da kamuwar su ba.

Acewar Kwamishinan gwamnatin Jihar ta samar da magunguna kyauta domin kula da masu dauke da cutar a cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko a Kananan hukumomi 11 na jihar.

Dr Habu ya ce daga cikin alamomin cutar sun haɗa da zazzabi, ciwon wuya, da ciwon kai mai tsanani, inda ya yi kira ga mutane da su dunga tsaftace muhallansu, kaucewa zama a gurare marasa iska, da kuma nisantar masu alamomin cutar domin hana yaduwarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: