Gwamnan Jihar Edo Sanata Monday Okpebholo ya yi Allah-wadai da kashe wasu mutane matafiya 16 wadanda suka kasance mafarauta ne ta hanyar kone su a garin Uromi da ke Karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a Jihar a jiya Alhamis.

Rahotanni shun bayyana cewa mutane da aka kashe ‘yan Arewa ne da suka taho daga garin Fatakwal na Jihar Rivers kuma suke kan hanyarsu ta dawowa Kano domin gudanar da bukuwan Sallaha, inda mazauna yankin suka hallaka su kan zargin cewa masu garkuwa ne, bayan samun su da makaman da suke gudanar da farauta.
A cikin wata sanarwa da babban jami’in tsaro na fadar gwamnatin Jihar Solomon Osaghale ya fitar a yau Juma’a, ya ce gwamnan ya nuna bacin bisa wannan danyen aikin da mutane suka aikata.

Gwamnan ya bayyana cewa kisan da aka yiwa mutanen rashin tausayi ne da ba zai amince dashi ba, yana mai cewa dukkan wanda aka kama da hannu a cikin kisan mutanen zai gurfana a gaban kotu domin fuskanci hukunci.

Fres Itua babban sakataren yada labaran gwamnan ya bayyana cewa a binciken da aka gudanar an gano cewa mutanen fasinjoji ne da ke cikin wata babban motar tirela da aka tsayar da ita.
Sakataren ya kara da cewa a bincike da jami’an tsaron sa-kai suka yi bayan sun tare su sun gano makamai a cikin motar, wanda hakan ya sanya zargi a zukatan mazauna yankin, kan cewa ‘yan bindiga ne, har ta kai ga sun rufar musu.
Acewar gwamnan babu wani wanda yake da ikon daukar mataki a hannunsa, inda ya ja kunnen mazauna Jihar da su kaucewa daukar doka a hannunsu, tare da tabbatar da zaman lafiya a Jihar.
Sannan gwamnan ya kuma bai’wa kwamishinan ‘yan sandan Jihar Umarnin gudanar da bincike, wanda hakan ya sanya aka kama mutame hudu daga cikin wadanda ake zargi da aika-aikaar.
Gwamna Monday ya shaidawa Hausawan yankin Uromi cewa jami’an tsaro sun dauki matakin tsare rayuka da dukiyoyinsu.
Shugaban al’ummar Hausawa na Uromi Aliyu Haruna ya yaba da matakin gaggawa da gwamnan ya dauka kan lamarin.
