Kungiyar gwamonin Arewa ta yi tir da kisan mutane 16 da aka yiwa wasu mutanen yankin a Jihar Edo.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahya ne ya yi Allah-wadai da lamarin ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ibrahim Uba Misalli ya fitar a yau Juma’a.
Sanarwar ta ce bayyana cewa kisan mutanen ya sabawa doka da saba hakkin dan Adam, wanda ba za a lamunta da shi ba.

Gwamnan Yahya ya ce aika-aikar na barazana ga doka da oda, kuma kowane dan Najeriya na da ‘yancin tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da tsoro ko wata barazana ba.

Kungiyar ta gwamonin ta ce ta damuwa matuka kan kisan mutane, inda ta ce ya zama wajibi a gano wadanda suka aikata kisan tare da kama su, da gurfanar da su gaban kotu cikin gaggawa, don hana sake faruwar hakan anan gaba.
Sanarwar ta gwamonin yankin na Arewa ta bakin shugabansu Muhammad Inuwa Yahya sun mika sakon jaje tare da ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu.
