Wani rikici da ya barke tsakanin bangarorin wasu ‘yan bindiga a Jihar Zamfara, ya yi sanadiyyar mutuwar wani hatsabibin dan bindiga Kachalla Isuhu Yellow ya rasa ransa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin jiya Alhamis, bayan Kachalla ya shafe tsawon lokaci ya na tserewa jami’an tsaro, da wasu jagororin ‘yan ta’addan.
Wani dan jarida mai gudanar da bincike kan sha’anin ’yan bindiga Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da hallah Yellow.

Yellow dai na aikata ta’addanci shi ne a yankunan Tsafe da Dan-Sadau a Jihar.

Sai dai mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama, ya bayyana cewa Isuhu Yellow ya rasa ransa ne a yayin wani hari da jami’an sojin Operation Fansar Yamma suka kai.
Makama ya ce Isuhu Yellow ya dauki tsawon shekaru yana aikata ta’addanci a sassan Zamfara, Katsina, da kuma wasu bangarori na Jihar Kaduna.
Acewar Makama Dan bindiga da ya kware wajen hallaka mutane, ya jagoranci kai hare-hare daban-daban, yin kwanton bauta ga jami’an tsaro, tare da garkuwa da mutane da shanu.
