Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na lll ya bukaci al’ummar musulmi da su fara duban watan Shawwal a gobe Asabar 29 ga watan Ramadan na shekarar 1446 dai dai da 29 ga watan Maris 2025.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin harkokin addini a Masarautar Sokoto, wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa dukkan wanda ya ga watan na Shawwal a gobe Asabar, da ya kai rahoto ga Hakimi ko kuma Dagacin mafi kusa don sanar da Sarkin Musulmi.

Sanarwar ta kuma yi addu’ar neman taimakon Allah a cikin aikin da za su gudanar.

