Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da gwamnan Jihar Edo Sanata Monday Okpehholo sun kai ziyarar ta’aziyya garin da mafiya yawa daga cikin mafarautan da aka kashe a Jihar Edo suka fito.

Gwamnan sun kai ziyarar ne a jiya Litinin, bayan gwamnan Jihar ta Edo ya zo Kano domin yin ta’aziyya ga gwamnan Kano da al’ummar Jihar kan kisan da aka yiwa Mafarautan.

A ziyarar gwamnan Abba, da gwamna Monday sun je garin Torankawa da ke Kano don yin ta’aziyyar mafarauta 16 da aka yiwa kisan Killa a Edo.

A yayin ziyarar gwamnan Gwamnan na Kano ya shaidawa ‘yan uwa da iyalan wadanda aka kashe cewa za a tabbatar da ganin an hukunta dukkan wadanda aka kama da hannun a cikin kisan.

Sannan gwamnan Abba ya ce gwamnatin Jihar ta Edo za ta yi kokarin ganin an biyasu diyyar ‘yan uwan na su.

Gwamna Abba ya kara da cewa za kuma a tabbatar da shaidawa duniya mutanen da suka yi aika-aikar tare da hukunta su don zama izina ga wasu.

Shima gwamnan na Edo ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da ganin an yi adalci a cikin lamarin, nan bada jimawa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: