Kotun Ƙolin ta Kasa ta soke hukuncin da Kotun daukaka Ƙara da ke Abuja ta yi na amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour Party na Kasa.

A hukuncin kotun Kolin a yau Juma’a, mai kwamitin alkalai biyar, ya bayyana cewa Kotun daukaka Ƙara ba ta da hurumin da za ta yanke hukunci akan bai’wa Abure shugabancin jam’iyyar ta Labour.

Alkalan kotun sun ce batun shugabancin jam’iyyar lamarin ne da ya danganci cikin jam’iyyar, inda kotu ba ta da hurumin yanke hukunci akai.

Kotun ta kara da cewa wa’adin shugabancin Abure a cikin jam’iyyar ya kare a hukumance, inda kotun ta amince da karar da Sanata Ester Nenadi Usman tare da wani mutum suka shigar gabanta.

Amma kotun ta yi watsi da karar da tsagin Abure ya shigar, tana mai cewa karar ba ta da wani amfani.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: