Dan takarar shugaban Kasa a jam’iyya PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta jita-jitar cewa ya fice daga jam’iyyarsa ta PDP.

Mai magana da yawun Atiku Paul Ibu ne ya musanta batun ta cikin wata wallafa da ya fitar a jiya Juma’a.
Alhaji Atiku ya bayyana hakan ne bayan hangan wata wallafa da yayi a shafin Facebook, na zargi Atiku da fice daga jam’iyyar ta PDP.

Sai dai bayan bullar wallafar, kakakin Atiku Ibe ya musanta zargi, yana mai bayyana cewa wallafar ko kadan babu kanshin gaskiya a cikinta.

Yana mai bayyana cewa wani abu ne na siyasa da aka shirya don kawo ruɗani da kuma yaudarar ‘yan Najeriya.
Atiku ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin jita-jitar, kuma an yi hakkan ne domin bata masa suna a siyasa, inda ya bukaci mutane da su yi watsi da batun