Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata motar haya mallakin kamfanin Benue Links a yankin Ikobi da ke cikin Karamar hukumar Otukpo ta jihar Benue, inda maharan suka hallaka direban motar da wani fasinja.

Inda kuma maharan suka yi garkuwa da sauran fasinjojin da ke cikin motar.
Rahotannin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a kusa da tsohon kamfanin Benue Burnt Bricks.

Motar wadda mallakin kamfanin gwamnatin jihar ce, maharan sun kuma kai mata hari a lokacin da take kan hanyarta ta zuwa Makurdi zuwa Otukpo.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Johnson Ehi Daniel ya fitar a jiya Juma’a, ya tabbatar da faruwar harin.
Kakakin ya kuma yi jinjina tare da yabawa da saurin daukar matakin gaggawa daga hukumomin tsaro.
A wata sanarwa da Rundunar ‘yan sandan jihar Catherine Anene ta fitar a jiya Juma’a, ta ce an kubtar da fasinjoji 14 da ‘yan bindiga suka sace.
Anene ta ce maharan sun kai harin ne a kusa da Otukpo, inda suka hallaka direban motar da wani fasinja.
Ta ce bayan samun rahoton jami’an ‘yan sanda hadin gwiwa da ‘yan sa-kai na jihar suka nufi gurin, tare da bin bayan maharan suka yi musayar wuta har ta kai ga sun kubtar da mutanen da maharan suka sace.