Wasu da ake zargi mayaƙan Lalurawa ne sun hallaka ƴan sa kai 13 a jihar Kebbi.

An hallaka ƴan sa kai ɗin yayin da mayakan su ka kai hari a garin Marai da ke ƙaramar hukumar Augie ta jihar.

Rahotanni sun ce jami’an sa kai ɗin sun yi kokarin dakile yunkurin maharan da su ka je garin da nufin satar shanu.

Wani mazaunin garin mai suna Malam Ibrahim ya bayyanawa wakilin jaridar Daily Trust cewar yan sa kai sun fita da nufin dakile harin sai dai maharan sun ci galaba a kansu har su ka hallaka 13 daga ciki.

Tuni mayakan su ka sace shanu da ba a kai ga gano yawansu ba.

Zuwa yanzu yan sanda a jihar ba su ce komai a kan lamarin ba.

Ana zargin mayaƙan Lalurawa da mamaye wasu yankunan dajin jihar Kebbi yayin da ake zargi sun bazu zuwa wasu jihohin arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: