Fadar shugaban Kasa ta musanta jita-jitar cewa shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC Farfesa Mahmood Yakubu daga kan mukaminsa.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da hadimin shugaba Tinubu kan sadarwar Daniel Bwala ya fitar a jiya Litinin.
Daniel ya bayyana cewa har yanzu Farfesa Mahmood Yakubu ne shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta Kasa INEC.

Hadimin na Tinubu ya ce irin wadandanan rahotannin wasu batagarin mutane ne marasa kishi ke kirkirarsa, wanda ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsu.

Daniel Bwala ya bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da bata da tushi balle makama.