Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da mutuwar mutane Takwas bayan tashin wani bom da ake zargin mayakan boko-haram ne suka da sa shi akan hanyar Maiduguri zuwa Damboa a Jihar.

Lamarin dai ya faru ne a jiya Asabar, kuma yayi sanadiyyar Jikkatar wasu da dama.
A yayin wata ziyarar da gwamnan Zulum ya kai’wa waɗanda suka jikkata a babban asibitin garin Maiduguri, ya bayar da umarnin yi musu magani kyauta.

Sannan gwamnan ya kuma bai’wa kowanne guda daga cikinsu kyautar Naira dubu 50.

Acewar gwamnan Zulum tashin bom din da aka samu akan hanyar hakan ba zai sanya a sake rufe hanyar ta Maiduguri zuwa Damboa ba.
Idan ba a manta ba a baya rundunar sojin Kasar nan ta rufe hanyar bisa matsalar rashin tsaro da ke faruwa a yankin, inda kuma daga bisani gwamnan Jihar ya bayar da umarnin bude ta, yayin da jami’an tsaro ke yiwa matafiyan da ke bin hanyar rakiya.