Gwamnatin Najeriya za ta hiras da ƴann jaridun yanar gizo da masu amfani fa kafofin sadarwa kan amfani da hanyoyin yada labarai na zamani.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris shi ne ya bayyana cewa ma’aikatarsa za ta fara horar da ‘yan jaridun yanar gizo kan sabbin hanyoyin yaɗa labarai da kuma amfani da fasahar zamani.


Ministan ya bayyana haka ne a saƙon godiya da ya aika wa mahalarta taron farko da aka yi da ‘yan jaridun yanar gizo da masu amfani da kafofin sa da zumunta na zamani na Arewacin Najeriya a ranar Laraba a Abuja.
Ya bayyana jin daɗinsa kan yadda taron ya gudana, inda aka samu musayar ra’ayoyi da shawarwari masu amfani daga mahalarta.
Ministan ya jaddada cewa irin wannan zaman za a ci gaba da gudanar da shi kafin ƙarshen shekara.
Alhaji Idris ya kuma ce za a riƙa ɗaukar wasu daga cikin mahalarta taron don basu horo na musamman a kan fasahohin zamani ciki har da ilimin ƙirƙirarriyar fasaha wato Artificial Intelligence, wanda ma’aikatar za ta shirya.
Sannan ya ce makamancin wannan taro za a shirya shi ga ‘yan jarida daga Kudancin Najeriya a nan gaba.