Wasu jami’an Hukumar Hana sha da fataucin miyagun Ƙwayoyi ta Kasa NDLEA sun tsallake wani harin wasu ɓatagari da suka kai musu ta hanyar buɗe musu wuta a yayin da suka kama miyagun ƙwayoyi a wani yanki na Abuja.

Mai magana da yawun hukumar na Kasa Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, inda ya ce wasu jami’ansu uku sun kubta da harbin bindiga inda a halin yanzu suke kwance a Asibiti ake kula da lafiyarsu.
BabaFemi ya ce an kai’wa jami’annasu harin ne a unguwar Jahi, a lokacin da suka kama wasu miyagun ƙwayoyi a ranar Alhamis.

Acewarsa lamarin ya faru ne bayan wasu bayanan sirri da jam’an suka samu, tare da kai sumamae a wani kwangon gini a yankin NNPC da ke unguwar ta Jahi, wanda hakan ya basu nasarar kwato kwalabe codeine 74, da codeine na ruwa lita 10, sai gram 48 na tramadol mai milligram 225, da kilogiram 4.9 na wani nau’in tabar wiwi, da kuma kwayoyin android biyar.

Kakakin ya kara da cewa a lokacin da jami’an nasu ke kan hanyarsu ta fitowa daga gurin, aka kai musu harin.
Har ila yau ya ce a halin yanzu jami’annasu da ke Asibi na samun kulawar gaggawa a asibitin ’yan sanda da ke Garki Area 1 kafin mayar da su Babban Asibitin Abuja domin kara samun kulawa.
Shugaban Hukumar Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa Mai Ritaya ya jinjinawa ma’aikatan asibitin na ’yan sanda bisa bayar da agajin gaggawar da suka bayar.