Mataimakin gwamnan Jihar Bauchi Auwal Jatau ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa ya mari Ministan harkokin cikin gida Yusuf Tuggar.

Jita-jitar dai na nuni da cewa lamarin ya faru ne a Jihar, bayan wani musayar yawu da ya barke tsakanin Ministan da nataimakin gwamnan a jiya Juma’a wadda ya kai ga mataimakin gwamnan ya mari Ministan.
Jita-jitar ta kara da cewa hakan ya samo asali ne bayan cin fuskar gwamnan da Ministan yayi, a lokacin da suke cikin mota wadda ke dauke da manayan jami’an gwamnati daga filin sauka da tashin jiragen sama na Jihar zuwa fadar sarkin Bauchi.

Manyan jami’an da suka je Jihar ta Bauchi wanda ciki harda mataimakin shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima sun je Jihar ne domin halaryar nadin sarauta ga tsohon gwamnan Jihar Mohammed Abubakar a matsayin Makama babba na daya, da kuma daura auren ‘yar tsohon gwamnan Khadija Muhammad.

Sai dai rahotanni sun ce bayan cin fuskar da Tuggar ya yiwa gwamnan, hakan ya sanya Jatau ya dauki matakin marin Ministan.
Sai dai a cikin wata sanarwa da kakakin Mataimakin gwamnan Muslim Lawal ya fitar, yace ba gaskiya ba ne faruwar lamarin.
Muslim ya ce babu yadda za a yi Mataimakin gwamna ya mari Minista ko wani mutum, yana mai cewa bashi da masaniya akan lamarin.
Kakakin gwamnan ya ce dukkan wanda ke da hujja akan hakan ya gabatar da ita, don tabatar da sahihanci lamarin.