Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya zargi tsohon Mataimakin shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar da rashin cika alƙawari.

Wike ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Baya ga Atiku Wike ya kuma sake zargin wasu manya a jam’iyyarsu ta PDP ciki har da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da gaza cika yarjejeniyar da suka yi a shekarar 2019.

Acewar Ministan marawa shugaban Kasa Bola Tinubu baya da yayi a zaben shekarar 2023 hakan shine abinda ya dace.

Ministan na Abuja ya kara da cewa duk da cewa jam’iyyar APC na cikin wani hali, bisa gazawar ta a lokacin gwamnatin tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari, amma duk da haka ya goyi bayan Tinubu duba da cewa yana ganin zai kawo sauyi a Kasar, tare da kallo Atiku a matsayin wanda ba mafita ba ga jam’iyyarsu ta PDP.
Kazalika Wike ya ce Atiku ya ci amanar yarjejeniya da suka kulla a 2019, shi da Bukola Saraki da kuma tsohon shugaban jam’iyyar ta su ta PDP na ƙasa Uche Secondus.
Wike gazawar Atiku wajen cika yarjejeniyar da suka kulla ne ya sanya ya yi watsi da shi, a matsayin wanda zai marawa baya, tare da yanke shawarar goyon bayan shugaba Tinubu.