Wasu jami’an tsaron Sa-kai biyar a Jihar Neja sun hallaka wani matashi mai suna Muhammad Omaba ta hanyar dukansa akan wata mace.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya tabbatar da hakan a yau Asabar ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Wasu Majiyoyi sun shaidawa Zagazola cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, inda aka tabbatar da mutuwar Omaba da ke zaune a ƙauyen Cuderegi da ke a ƙaramar hukumar Lemu Gbako ta jihar.

Jami’an sa-kan da ake zargi da aika-aikar su hada da Alhaji Yikangi, Modu Alhaji Idris, Danjuma Yikangi, Worongi Yikangi, da kuma wani da ake yiwa lakabi da Mai Tawhidi.

Dukkan wadanan mutane biyar din na a wata Ƙungiyar tsaron Sa-kai da ke aikin a cikin Ƙauyen, inda suka kai’wa farwa Omaba da misalin karfe 1:00 na daren ranar.
Majiyoyin sun ce lamarin ya fara ne da wata cacar baki da ta faru a tsakaninsu kan wata mata mai suna Fatima Suleiman da ta kasance itama mazauniyar ƙauyen na Cuderegi ce.
Hakan ya sanya cacar bakin ta koma rigima, inda suka rufe Omaba da duka har ya suma, inda aka kai shi Asibiti Lemu don ba shi a gajin gaggawa, daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Bayar faruwar lamarin jami’an ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike, tare fara neman waɗanda ake zargi domin tare da gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.