Aƙalla mutane shida ne du ka mutu yayin da wasu da dama su ka jikkata a wani rikici da ya ɓarke tsakanin mutanen Benue da Ebonyi.

Wasu da ake zargi sun fito ne daga Ebonyi sun abkawa mutanen ƙauyen Ezza da ke ƙaramar hukumar Ado ta jihar Benue.

An fara sabon rikicin ne a yammacin jiya Asabar wanda wasu yan bindiga du ka buɗe wuta.

Wata majiya ta ce mutane na tsaka da harkokinsu sai wasu mayaƙan Effium su ka far musu bayan yi musu dirar mikiya.

Sakamakon haka mutane shida sun rasa ransu yayin da wasu da dama su ka jikkata.

Sau dai zuwa wannan lokaci Yan sanda a jihar ba du ce komai a kai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: