Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya bayan shafe makonni biyu a tafiya da ya yi zuwa ƙetare.

A wata sanarwa da hadimin shugaban Bayo Onanuga ya sanyawa hannu, ya ce shugaba Tinubu zai dawo Najeriya yau Litinin.

Kafin dawowar, shugaban ya zarce Burtaniya bayan ziyarar aiki da ya kai Faransa.

Tafiyar da shugaban ya yi an ta yaɗawa cewar, shugaban ya je ne domin a duba lafiyarsa, sai dai fadar shugaban ƙasa ta musanta.

Ko da cewar shugaban ya ƙara a kan kwanakin da ya ɗauka, sai dai ya ci gaba da ayyukansa tare da bayar da umarni ga muƙarrabansa don gudanar da ayyukansa.

Sanarwar ta kuma tabbatar da nuna godiya ga ƴan Najeriya bisa kuna damuwa da su ke yi kan halin da shugaban kasar ke ciki.

Shugaba Tinubu ya bar Najeriya a ranar 2 ga watan Afrilu kusan makonni uku kenan a ziyarar aiki da ya tafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: