Dillalan man fetur na a Najeriya na fargaban tafka asara bayan da kamfanin mai na ƙasar NNPC ya rage farashin kowacce lita.

Kamfanin ya sanar da dawo da kowacce lita naira 880 a Legas yayin da a Abuja ake siyarwa naira 935.

Rage farashin da kamfanin ya yi na zuwa ne mako guda da matatar mai ta Dangote ta rage farashin kowacce lita.

Kafin rage farashin da kamfanonin su ka yi, farashin danyen mai ya faɗi a kasuwar duniya.

Haka kuma gwamnatin Najeriya ta amince da ci gaba da siyarwa da matatun mai na cikin gida danyen mai a kuɗin naira.

Da yake tabbatar da rage farashin man, mataimakin shugaban ƙungiyar dillalan man fetur na Najeriya Hammed Fashola ya tabbatar da hakan.
Sai dai ya ce gidajen mai na iya tafka asara sakamakon rage farashin da aka yi.

Dangane da gidajen mai da ba su rage farashin litar man ba, ya ce tsohon mai ne da su ka siyoshi da tsada kuma da zarar sun siyar da shi za su rage farashin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: