Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aikewa da majalisar Dokokin Jihar takardar godiya bisa yadda Majalisar ke goyon bayan Majalisar zartarwa a koda yaushe.

Sannan gwamnan ya kuma shaidawa Majalisar cewa za a rushe ginin Majalisar domin gina sabon zauren Majalisar da yayi dai-dai da zamani.

Gwamnan ya aike da wasikar ne a zaman Majalisar na yau Talata, inda kuma ya bai’wa Majalisar umarnin samarwa kanta mazauni na wucin gadi.

Shugaban Majalisar Hon Isma’il Falgore ne ya karanta takardar gwamnan a zaman Majalisar na yau, bayan dawowa daga dogon hutun da ta tafi.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: