Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta kama wani Buhari Sule mai shekaru 25 a duniya bisa zargin hallaka matar ƙaninsa.

An kama Buhari a ƙauyen Gunka da ke ƙaramar hukumar Jahun a jihar
Wanda ake zargi da hallaka abokiyar mahaifiyar tasa ana zargin ya na da taɓin hankali.

An kamashi a yammacin jiya Laraba bayan sanar da jami’an yan sanda.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Lawal Shiisu Adam ya ce matashin ya yi amfani da taɓarya wajen hallaka matar ƙanin nasa.
Baya ga Ummi Saleh da ya halaka akwai wata yarinya Hauwa Alkasim mai shekaru shida wadda ya yi wa rauni.
Tuni ƴan sanda a jihar su ka duƙufa don bincike a kan lafiyar ƙwaƙwalwarsa wanda daga nan za a dauƙi mataki na gaba.
