Gwamnatin Tarayya ta bayaanna cewa ba za ta iya ci gaba da biyan naira Biliyan 47 a kowacce shekara a matsayin kudin wutar lantarkin fadar shugaban Kasa ba.

Darakta a hukumar Makamahi ta Kasa Mustapha Abdullahi ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a wata ganawa da manema labarai, yana mai cewa gwamnatin ta tarayya za ta yi hakan ne domin rage kudin da ta ke kashewa duk shekara a bangaren lankarkin fadar shugaban Kasa.
Acewarsa hakan ne ya sanya shugaban Kasa Bola Tinubu ya amince da fitar da naira biliyan Goma domin sanya Sola mai amfani da hasken rana fadar shugaban Kasar.

Daraktan ya kara da cewa matakin na cikin shirye-shiryen shugaba Tinubu na bunƙasa hanyoyin samar da makamashi da rage kuɗin gudanarwa.

Mustapha ya ce samar da tashar ta Sola a fdar shugaban Kasa hakan zai sanya a samar da wuta mara yankewa da tsafta, da samar da ayyukan yi, da bunƙasa ƙwarewar injiniyoyi da masana makamashi na Najeriya.
Kazalika ya ce shirye-shiryen gwamnatin tarayya a yanzu sun sanya masu zuba hannu jari na ƙasashen ketare ware daa biliyan 5.3 domin saka jari a harkar wutar lantarki.