Ma’aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya sun janye daga yajin aikin da su ka tsunduma.

Wannan ya biyo bayan zaman da ministan sufurin jiragen sama na ƙasa Festus Keyamo ya yi da su jiya Alhamis.

Ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin ne sakamakon rashin aiwatar da mafi karancin albashi da kuma gaza biyansu hakƙokinsu.

Sakamakon yajin aikin da su ka tsumdumaa ya sanya kamfanin jirgi na Air Peace ya dakatar da ayyukansa a Najeriya baki daya.

Sai dai sun bayyana janyewa daga yajin aikin bayan zaman da su ka yi da ministan.

Kwanaki biyu su ka shafe su na yajin aikin wanda hakan ya haifar da tsaiko musamman ga masu son yin tafiya a jirage a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: