Ƙasar Tanzaniya ta ɗage dakatarwar da ta yi na shiga da kayan amfanin gona zuwa ƙasar daga ƙasashen Malawi da Afirka ta Kudu, an bayyana hakan a jiya Juma’a awanni kaɗan bayan sanya takunkumin.

Gwamnatin ƙasar Tanzaniyan dai ta sanya takunkumin ne a matsayin mayar da martani, daidai da irin matakan da ƙasashen biyu su ka sanya a kan ta.

Shugaban hukumar tabbatar da lafiyar amfanin gona da magance ƙwari Joseph Ndunguru ya bayyana cewa, ƙasar Tanzaniyan ta janye dakatarwar ne nan ta ke domin bayar da damar tattaunawa bisa tsarin diplomasiyya, sakamakon tuntuɓar su da ƙasashen biyu su ka yi don buƙatar kawo ƙarshen taƙaddamar harkokin kasuwanci.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai ministan harkokin noma na ƙasar Tanzaniya ya dakatar da shigar da duk wasu kayan amfanin gona daga ƙasashen Malawi da Afirka ta Kudu zuwa ƙasar, tare kuma da dakatar da fitar da takin zamanin da su ke sarrafawa zuwa ƙasar Malawi, wanda ta dogara a kai kacokam.

A ɓangarensu ministan hulɗar ƙasashen duniya na Afirka ta Kudu Ronald Lamola ya yi farin ciki dangane da ɗage takunkumin, ya ce hakan zai haɓaka ƙaƙƙarfar alaƙar ƙasashen biyu.

Tun da fari dai ƙasar Malawi ce ta fara dakatar da shigar da kayayyakin amfanin gona daga ƙasar Tanzaniya zuwa cikinta, kamar su masara, shinkafa, citta, fulawa da sauransu, yayin da ita ma ƙasar Afirka ta Kudun ta dakatar da shigar da ayaba zuwa ƙasar daga Tanzaniyan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: