Ƴan Bindiga sun hallaka mutane 10 ciki har da jami’in ƙungiyar bayar da kariyar tsaro ga al’umma wato Murtala Fachi, a cikin wasu hare-haren da aka kai jihar Zamfara.

An dai kashe Murtala Fachi ne tare da wasu fasinjoji mutane biyu, yayin da su ke tafiya akan hanyar titin Anka zuwa Gusau a makon da mu ke ciki.

An bayyana cewa jami’in na han hanyar sa ne ta zuwa Gusau domin bayar da shaida a gaban kotu akan wata shari’a, lokacin da yan bindiga su ka ƙone ababen hawansu a kusa da Tashan Kuturu, wani sanannen waje mai hatsari a kan hanyar Anka zuwa Mayanchi.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa ƴan bindigar sun buɗe wuta ne akan abin hawan, inda nan ta ke su ka hallaka matuƙin da kuma fasinjoji guda biyu ciki har da Fachi.

A wani lamarin kuma makamancin wannan, an hallaka mutane bakwai a wani harin na daban da aka kai Dolen Moriki da ƙauyen Kaiwa Lamba, a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar.

Dukka hare-haren dai sun faru ne da safiyar Talatar makon da mu ke ciki, inda mazauna yankin su ka bayyana lamarin a matsayin mai sanya kaɗuwa sosai.

Sai dai har zuwa yayin kammala tattara wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ta Zamfara DSP Yazid Abubakar ba, domin ya yi ƙarin bayani da tabbatar da afkuwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: