Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC Joe Ajaero ya koka dangane da illar hauhawar farashin kayayyaki ke yi akan sabon tsarin mafi ƙarancin albashi.

Ajaero yayin da ya ke jawabi a wajen taron ƙungiyar ƴan kasuwa jiya Juma’a a birnin tarayya Abuja, ya ce lokaci ne da ya kamata ƙungiyoyin su haɗe kansu su tsaya tsayin daka wajen yaƙar matsalolin da su ke addabar ma’aikata.

Ya kuma ƙara da cewa yanzu haka ƴan Najeriya su na biyan kudin wutar lantarki da haraje-haraje fiye da sabon ƙarin albashin na dubu 70, wanda gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta amince da shi.

Ajaero ya ce sun yi fafutuka sosai akan tsarin ma fi ƙarancin albashin kuma ba su gajiya ba, sun kuma yi yaƙi da janye tallafin man fetur kuma yanzu haka su na yi akan ƙarin haraji.

Ya kuma ƙara da cewa duk ƙarin da aka sahale a matsayin mafi ƙarancin albashi, tuni ana zaizaye shi ta hauhawar farashin kayayyaki da kuma haraje-haraje, tare da cewa rayuwa ta yi tsanani sosai.

Inda kuma ya ce ƙalubalen da ma’aikata su ke fuskanta gaskiya ne ba da gangan ba ne, kuma su na buƙatar jajantacciya kuma ƙaƙƙarfar ƙungiyar ƴan kasuwa don magance su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: