Shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya WTO wato Ngozi Okonjo Iweala ta bayyana cewa, ƙarin tsarin haraji da gwamnatin Amurka ta wanzar ba zai yi wani babban tasiri ga ƙasashen Afirka ba.

Ngozi ta bayyana hakan yayin zantawa da ƴan jaridun Najeriya a wajen babban taron bankin duniya, da ya gudana a birnin Washington DC da ke Amurka a jiya Juma’a.
Ta kuma ce iya kashi 6.5 cikin 100 ne na kayayyakin da nahiyar Afirka ke shigowa da shi ya ke zuwa ga ƙasar Amurka, yayin da kashi 4.4 cikin 100 na kayan da ta ke fitarwa ke zuwa daga Amurka, saboda haka tasirin ƙarin harajin ba shi da wani girma.

Okonjo ta ce kasuwancin nahiyar tare da Amurka ba shi da wani girma sosai, kuma sun yi hasashe da ƙididdiga akan batun, saboda haka ba za a samu wani tasiri ba na azo a gani.

Babbar daraktar ta kuma ce akwai bukatar nahiyar Afirka ta mayar da hankali wajen amfani da kayayyakin ta na gida don cimma ga ci, saboda yanzu an daina bayar da tallafi kuma nahiyar na buƙatar saka hannun jari sosai.
Ngozi ta kuma ce nahiyar Afirka ta na kashe kimanin Dala miliyan dubu 700 wajen shigo da kayayyakin sawa a kowacce shekara, inda ta ce ƙasa kamar Lesotho ya kamata ta mayar da hankali wajen siyar da kayayyakin sawa a cikin kasuwannin Afirka.
A ƙarshe ta kuma buƙaci ƙasar Amurka da ta yi duba da illar da ƙarin haraji zai yi wa kasashe masu tasowa, tare da sake duba da tsarin ƙarin harajin akan ƙasashe marasa ƙarfi.