Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce ba zai shiga ƙungiyar haɗakar siyasa ta ƴan jam’iyyar adawa ba, wacce tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya ke jagoranta.

Jawabin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Mamman Muhammad ya fitar, a jiya Asabar a birnin Damaturun jihar ta Yobe.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito yadda wani saƙon ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda saƙon ke ɗauke da cewa gwamna Bunin tare da wasu gwamnoni huɗu sun kammala shirinsu na komawa jam’iyyar hamayya ta PDP kafin lokacin zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Muhammad ya bayyana saƙon a matsayin ƙirƙirarre marar tushe ballantana makama, wanda ko kadan bai yi kama da hankali da gaskiya ba.

Ya kuma ƙara da cewa wanda ya ƙirƙiro saƙon bashi da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da gwamnan, ballantana har ya iya yin hasashen tsarin tafiyar da siyasarsa.
Muhammad ya kuma ce gwamna Buni ba wai irin sauran gama-garin ƴan jam’iyyar APC ba ne, ta ko ina shi ɗan jam’iyyar APC ne a jini da tsokar jikinsa.