Babban ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya umarci da a rufe asibitocin da su ke ba bisa ka’ida da kuma haramtattun jami’an lafiya a faɗin birnin tarayya Abuja.

Babban mai taimakawa ministan a ɓangaren sadarwa Lere Olayinka ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja a ƙarshen makon nan.

Olayinka ya ce ministan ya bayar da umarnin ne yayin da ya ke tsokaci dangane da mutuwar wata mata mai dauke da juna biyu, a wani asibiti mai zaman kansa da ke Durumi a Abuja, biyo bayan yi mata aiki.

Ya kuma bayyana cewa Wike ya yi gargaɗin duk wanda aka samu ya na aiki ba bisa ka’ida ba ko kuma a haramtattun asibitoci, a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Ya ce abin takaici ne duk da tsarin haihuwa kyauta na tsarin inshorar lafiya a birnin tarayyar, amman har yanzu wasu matan masu ɗauke da juna biyu ba sa ƙoƙarin amfana da shirin.

Ya ce a birnin na Abuja mararsa ƙarfi ciki har da mata masu juna biyu, a na shigar da su tsarin na inshorar lafiya kyauta, kuma hakan ya na basu damar cin moriyar tsarin kula da lafiya cikin sauƙi.

A ƙarshe ya yi kira da matan da su dinga yunkurin amfana da shirin, kuma su daina zuwa gurɓatattun asibitoci da haramtattun jami’an kula da lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: