Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za a sake buɗe filin sauka da tashin jiragen sama na Akanu Ibiam da ke jihar Enugu, a ranar 28 ga watan Afrilun nan da mu ke ciki biyo bayan gyaran da aka yi a hanyar saukar jiragen.

Mai magana da yawun hukumar kula da filayen jirgin sama Obiagheli Orah ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar.

A ranar 18 ga watan Afrilun nan ne dai hukumar kula da filayen jirgin saman ta sanar da rufe filin jirgin don yin wasu gyararraki, sakamakon lalacewar kwaltar da ke kan hanyoyin saukar jiragen a waje mai matukar hadari.

Orah ya bayyana cewa an kudiri aniyar fara yin aikin ne a ranar 22 ga watan Afrilun nan, tare da kammala shi kafin ranar sake buɗewa a ranar 6 ga watan Mayu.

Sai dai kuma tuni an kammala gyaran da ake yi a filin jirgin, kuma hanyoyin saukar jiragen sun zama ƙalau ba tare da wata matsala ba a yanzu haka.

Ya ce hukumar ta su tana matukar jinjina ga dukkan masu amfani da ma’aikatan filin jirgin, sakamon nuna fahimta, juriya da haƙurin da su ka yi da bayar da haɗin kai har aikin ya kammala.

A ƙarshe ya ce hanyoyin saukar jiragen da aka gyara su na kawo matsaloli wajen saukar jiragen, ko kuma ma a dakatar ko sauya akalar saukar jirgin zuwa wani filin baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: