Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar lll, ya bayyana gobe Talata a matsayin 1 ga watan Zulƙida na shekarar 1446, daidai da 30 ga watan Afrilu 2025.

Shugaban kwamatin ganin wata na fadar Sarkin Musulmin Farfesa Sambo Wali ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin.
Sanarawr ta bayyana cewa bisa rashin ganin wata da ba a yi ba a jiya Lahadi, hakan ya nuna gobe Talata ne 1 ga watan na Zulƙida.

Sanarwar ta kara da ce a yau Litinin wata Shawwal ya cika kwanaki 30, yayin da gobe Talata ya kasance 1 ga sabon watan na Zulƙida.
