Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aikewa da Majalisar dokokin Jihar, wasikar neman amincewa da AVM Umar Ibrahim a Matsayin guda daga cikin ‘yan Majalisar zartarwar Jihar.

A zaman Majalisar na yau Litinin, shugaban Majalisar Hon Isma’il Falgore ne ya karanta da wasikar da gwamnan ya aikewa da Majalisar.
Bayan Karanta takardar gwamnan a gaban zauren Majalisar, Majalisar ta aike da gayyata ga AVM Umar Ibrahim domin tantance shi.
Majalisar ta shaida cewa za ta tantance AVM Umar ne zamanta na gobe Talata.

Hadimin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Bashir Ahmad, ya musanta zargin da Sanata Solomon Adeola ya yiwa tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari na cewa ta karɓo bashin dala biliyan 400 domin farfado da darajar Naira a Kasar.
