Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aikewa da Majalisar dokokin Jihar, wasikar neman amincewa da AVM Umar Ibrahim a Matsayin guda daga cikin ‘yan Majalisar zartarwar Jihar.

A zaman Majalisar na yau Litinin, shugaban Majalisar Hon Isma’il Falgore ne ya karanta da wasikar da gwamnan ya aikewa da Majalisar.

Bayan Karanta takardar gwamnan a gaban zauren Majalisar, Majalisar ta aike da gayyata ga AVM Umar Ibrahim domin tantance shi.

Majalisar ta shaida cewa za ta tantance AVM Umar ne zamanta na gobe Talata.

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: