Tsohon gwamnan Jihar Delta Ifeany Okowa ya bayyana cewa ya yi dana sanin yiwa dan takarar shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, takarar mataimakin shugaban Kasa a zaben 2023 da ya gabata.

Okowa ya bayyana hakan ne a yau Talata, a wata hira da Arise TV.
Acewarsa amicewa da yayi zai yiwa Atiku takarar mataimakin shugaban Kasa a zaben na 2023, hakan ya sabawa muraden al’ummar Jiharsa ta Delta.

Okowa ya kara da cewa yiwa Atiku takarar Mataimakin shugaban Kasa da ya yi, hakan ya haifar masa da babbar asara a siyasa.

Tsohon gwamnan na Delta na wannan kalami ne mako guda da ficewarsa daga jam’iyyar ta su ta PDP zuwa APC, inda a jiya Litinin jam’iyyar ta APC ta gudanar da bikin karbarsu a hukumance.