Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta kama mutum guda da ake zargi da hannu a hallaka tsohon shugaban Karamar hukumar Jama’are Isa Wabi a Jihar.

Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, ta ce an hallaka tsohon shugaban Karamar ne a gidamsa da ke garin Madaman Mada a cikin daren yau Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda ake zargin da yin aika-aikar abokai ne ga ɗan Marigayin Abdulgafar Isa Mohammed, inda kuma suka hallaka shi ta hanyar caka masa Wuƙa a wuyansa.

Rundunar ta ce bayan faruwar lamarin jami’ansu sun isa gidan Marigayin, tare da kai shi Asibitin Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Jihar.

Runduanar ta kara da cewa a binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa wasu mutane biyu ne ake zargi da aikata laifin.
Acewar sanarwar tuni rundunar ta kama ɗan Tsohon shugaban Ƙaramar hukumar domin ci gaba da faɗaɗa bincike kafin daukar mataki na gaba.