Rundunar ’yan sandan birnin tarayya Abuja ta tabbatar da kama mutane 1,611 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a fadin Kasar.

Kwamishinan ’Yan sandan birnin Ajoa Saka Adewale ne ya tabbatar da hakan a yau Juma’a a Abuja a okacin da yake holan kayan laifin da aka ƙwato a gaban manema labarai.
Kwamishinan ya ce mutanen da ta kama sun haɗa da masu safarar miyagun ƙwayoyi, da ƙwato motocin sata 21, babura 51 da kuma miyagun ƙwayoyi da dai sauransu.

Adewale an kama mutane 16 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban na satar mota, ya yin da kuma shida daga cikin motoci 21 da aka ƙwato an mayar da su ga masu su bayan kammala bincike, inda sauran motocin 13 ke hannun rundunar.

Acewarsa nasarar na samu ne a samame daban-daban da suka kai gurare da dama.
Kwamishinan ya kara da cewa da yawa daga cikin mutane na da alaƙa da laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.
Kwamishinan ya ce an kuma gano wani adadi mai yawa na miyagun ƙwayoyi na tabar wiwi, inda ya ce bayan sun kammala gudanar da bincike za a gurfanar da dukkan wadanda aka kama a gaban kotu domin girbar abinda suka shuka.