Babbar Kotun Jihar Ekiti ya yankewa wani matashi mai suna David Isaiah mai shekaru 26 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kamashi da aka yi da laifin hallaka wata mace ta hanyar amfani da maganin kashe ciyawa bayan yin lalata da ita.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan gurfanar da aka yi da a gabanta bayan ya aikata laifin tun a ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata.
Mai gabatar da kara a gaban kotun Ibironke Odetola ya shaidawa kotun cewa wanda ake zargin ya hada baki ne da wani abokinsa gurin sace matar da ke yin kasuwanci.
Abin zargin ya shaidawa kotun cewa, bayan ya gama lalata da ita ya yi amfani da wayarta, tare da kiran abokan kasuwancinta da ya shaida musu cewa an sace ta, inda kuma ya nemi naira 100,000 a matsayin kudin fansa kafin sakinta.

Alkalin kotun mai shari’a Lekan Olatawura ne ya yanke masa hukuncin laifin masu garkuwa da mutane, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 21 bisa laifin hadin baki da kuma garkuwa.

Alkalin ya kuma ce a laifin kisa da David ya aikata kuwa an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.